(ABNA24.com) Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kakakin mayakan gwamnatin Tripoli Muhammad Qanunu ya fitar a yau, ya bayyana cewa dakarunsu sun samu nasarar fatattakar dakarun Haftar daga garin Tarhunah da ke kudancin birnin Tripoli.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, kafin wannan lokacin dakarun nasu sun samu nasarar kwace iko da garin Irban da ke hannun dakarun Haftar.
Ya ce za su ci gaba da korar dakarun Haftar da ya ce a halin yanzu sun janye daga kudancin birnin Tripoli, kuma za su ci gaba bin sawunsu a yankunan Muzdah, da Bani Walid da ke kudancin birnin.
Kafin wannan lokacin dai majalisar dinkin duiya ta sanar da cewa, dukkanin bangarorin gwamnatin Tripoli da kuma Haftar da suke yaki da juna a Libya, sun sanar da amincewa da komawa kan teburin tattaunawa da sulhu, amma Firayi ministan gwamnatin Tripoli Faiz Suraj da ke ziyara a Turkiya, bayan ganawarsa da shugaban kasar Turkiya a Rajab Tayyib Erdogan a jiya Alhamis, a yau Juma’a ya fito ya bayyana cewa babu batun sulhu tsakaninsu da Haftar.
Ana zargin shugaban kasar ta Turkiya Rajab Tayyib Erdogan da kashe dubban ‘yan ta’adda da suke yaki a Syria zuwa kasar Libya, domin yin yaki a cikin sahun dakarun gwamnatin Tripoli, domin yakar dakarun Haftar.
/129
6 Yuni 2020 - 05:53
Lambar labari: 1043648
Dakarun gwamnatin Tripoli a kasar Libya, sun sanar da kwace iko da garin Tarhunah daga hannun dakarun Haftar a yau Juma’a.